Home Labaru Ilimi Bayan Bincike: JAMB Ta Bayyana Ranar Da Za Ta Fitar Da Sakamakon...

Bayan Bincike: JAMB Ta Bayyana Ranar Da Za Ta Fitar Da Sakamakon Jarabawa

550
0

Hukumar Shirya Jarabawar share fagen Shiga Jami’a JAMB, ta tabbatar da cewa za ta fitar da sakamakon jarabawar wannan shekarar a ranar 29 ga watan Afrilu.

Jam’in Hulda da Jama’a na hukumar Fabian Benjamin ya bayyana haka, yayin wata jhira da ya yi da manema labarai a Abuja.

Ya ce ba da dadewa ba za a kammala yi wa sakamakon binciken kwakwaf, ta yadda za a sake shi ranar Litinin kowa ya ga abin da ya samu.

Da ya ke magana a kan bin diddigin sakamakon da za a yi na jarabwar shekara ta 2009 zuwa 2019 kuwa, Benjamin ya ce ba za a fara ba sai bayan an fitar da sakamakon shekara ta 2019 a mako mai zuwa.

Ya ce hukumar JAMB ta dauko gagarumin shirin ne domin a dakile satar jarabawa tare da kama masu satar jarabawa.

Tsarin dai,  zai zakulo wadanda su ka yi rajista sau biyu, tare da wadanda su ka yi rajistar bai-daya a wata makarantar ‘ya’yan masu hannu da shuni, wadanda a karshe su ke baddala bayanan sunayen masu rubuta jarabawa.

Leave a Reply