Wasu bata-gari sun kai hari a gidan rediyon Gwamnatin Jihar Kogi, inda su ka kone shi tare da yin awon gaba da kayayyakin sa.
Bata-gari sun afka wa tashar gidan rediyon da ke Ochaja a Karamar Hukumar Dekina harin ne a safiyar ranar Talatar da ta gabata, inda su ka lakada wa masu gadin wurin dukan kawo wuka, sannan su ka rika cin Karen su babu babbaka tare da kona muhimman kayayyaki.
Maharan dai sun sace duk muhimman kayyayakin da ke gidan rediyon, ciki kuwa har da wani janareto kirar Mikano da wani dan takarar gwamna ya bada gudummawa.
Tuni dai Gwamnatin Jihar Kogi ta yi Allah-Wadai da harin a cikin wata sanarwa da kakakin ma’aikatar yada labarai na jihar Salawu Patience ta fitar, amma ta bada tabbacin cewa jami’an tsaro su na aiki domin kamawa da kuma gurfanar da bata-garin a gaban kuliya.
Ta ce kwamishinan ma’aikatar Kingsley Fanwo, da shugaban hukumar yada labarai na jihar Alhaji Ojo Oyila Ozovehe sun ziyarci tashar domin ganin irin barnar da aka yi.