Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Bashin Noma: Rifan Za Ta Maka Manoman Shinkafa 113 Kotu A Jihar Kastina

Kungiyar manoman shinkafa ta Nijeriya reshen jihar Katsina RIFAN, ta ce za ta maka manoman shinkafa 113 da su ka ki biyan bashin kudade da kayan noman da shirin ‘Anchors Borrowers Program’ ya ba su.

Shugaban kungiyar da ke karamar hukumar Daura Nura Baure ya bayyana wa manema labarai haka a garin Daura, inda ya ce kungiyar za ta dauki matakin ne, ganin cewa manoman da su ka karbi bashin sun ki biya duk da tsawon lokacin da aka ba su domin su maido kudaden.

Ya ce daga yanzu kungiyar za ta dauki mataki mai tsauri a kan duk manomin da ya karbi kayan noma sannan ya ki biya.

Baure ya kara da cewa, kungiyar ta raba wa manoman Irin shinkafa da takin zamani da Goran Feshi da maganin feshi, da Injin Ban-Ruwa da sauran su.

Akalla manoma 5000 ne su ka yi rajista da wannan kungiya don samun tallafi, inda a karon farko kungiyar ta tallafa wa manoma dubu 3 da 500.

Exit mobile version