Home Labaru Ilimi Bashin Kudin Karatu: EFCC Ta Mika Wa NELFUND Naira Biliyan 50

Bashin Kudin Karatu: EFCC Ta Mika Wa NELFUND Naira Biliyan 50

55
0
EFCC LOGO jpg
EFCC LOGO jpg

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta mika wa asusun da ke ba da tallafin karatu na NELFUND Naira biliyan 50.

Cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, EFCC ta ce kudin na daga cikin kudaden da aka kwato daga masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ne,\

ta ce ba gudunmowa ba ne kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka ruwaito.

EFCC ta ce a kokarin sa na kai wa ga marasa galihu ne, Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yanke shawarar a saka kudaden a asusun ba dalibai bashin kudin karatu.

Ya zuwa yanzu NELFUND ya tantance jami’o’i, da kwaleji-kwaleji da sauran manyan makarantu a matakin jiha sama da 100 da za a fara ba bashin kudin karatun.

Leave a Reply