Home Labaru Bashin Ketare: Asusun Bada Lamuni Na Duniya Ya Gargadi Nijeriya

Bashin Ketare: Asusun Bada Lamuni Na Duniya Ya Gargadi Nijeriya

183
0

Asusun bada lamuni na Duniya IMF, da  Manyan kungiyoyin harkar tattalin arziki na Duniya, sun gargadi Nijeriya game da cin bashi a wasu kasashe.

Kungiyoyi sun bukaci Nijeriya da sauran kasashe su rika bi a hankali wajen karbar rancen kudi daga ketare, inda Asusun bada Lamunin ya nemi kasashe irin Nijeriya su rika duba ka’idojin da ake gindaya masu yayin da su ke neman cin bashi daga kasashen waje.

Wani babban jami’in Asusun bada Lamuni na IMF, ya shawarci Nijeriya da sauran kasashe masu tasowa su kara yawan harajin da su ke karba a cikin gida da ake kira Jiki Magayi wato VAT.

Tobias Adrian, ya ce akwai bukatar Nijeriya ta dage wajen samun kudin shiga ta hanyar hukumar yaki da fasa-kwauri.

Asusun IMF ya nuna cewa, babu wata matsala game da cin bashi daga kasar Sin, sai dai ya kamata kasashen da ke ciwo bashin su rika lura da sharuddan da ake gindaya masu don gudun shiga sarkakiya.