Home Labarai Bashi: Jahohi 21 Na Neman Karbo Kudi Fiye Da Tirilliyan Faya

Bashi: Jahohi 21 Na Neman Karbo Kudi Fiye Da Tirilliyan Faya

68
0
Nigerian Governors forum (1)
Nigerian Governors forum (1)

Jihohi 21 a Najeriya na neman ciyo bashin Naira tiriliyan daya da biliyan 650, duk kuwa da ƙarin kashi 40% da aka samu kuɗaɗen da suka samu daga Kwamitin Asusun Tarayya (FAAC) a shekara guda da ta gabata.

Bincike ya nuna cewa kashi 20% na kuɗaɗen FAAC na watan Yuni 2023 kaɗai (biliyan N160) zai gina cibiyoyin lafiya a matakin farko guda 320 a faɗin Najeriya.

Aminiya ta gano cewa tuni jihohin suka aike da takardunsu na neman ciyo bashin daga ƙasashen waje da kuma cikin gida. Ragowar jihohin kuma ba su bayyana nasu ba, game da ciyo bashi ko akasin haka.

Jerin jihohin da yawan bashin da kowaccen su ke neman ciyowa su ne, Adamawa – Biliyan N68.46. Anambra – Biliyan N245. Bauchi – Biliyan,

,N59.08. Bayelsa – Biliyan N64. Benue – Biliyan N34.69. Borno – Biliyan N41.71. Ebonyi – Biliyan N20.5. Edo – Biliyan N42.71. Ekiti – Biliyan,

N27.15. Jigawa – Biliyan N1.78. Kaduna – Biliyan N150.1. Kebbi – Biliyan N36.7. Katsina – Biliyan N163.87. Kogi – Biliyan N37.08. Kwara – Biliyan N30.76.,

Osun – Biliyan N12.36. Oyo – Biliyan N133.4. Nasarawa – Biliyan N32.93. Gombe – Biliyan N73.75. Enugu – Biliyan N103. Imo – Biliyan N271.34.

Gwamnatocin jihohi 21 da ke neman wannan bashin na Naira tiriliyan 1.65 sun ce za su yi amfani da kuɗaɗen ne wajen cike giɓin da suka samu a kasafin kuɗinsu na shekarar 2024 da muje ciki.

Leave a Reply