Home Labaru Barkewar Rikici: An Sanya Dokar Hana Fita A Gombe

Barkewar Rikici: An Sanya Dokar Hana Fita A Gombe

333
0

Gwamnatin jihar Gombe, ta sanya dokar hana fita a birnin Gombe, biyo bayan rikicin da ya barke yayin da ake rufe gawarwakin wasu matasa tara ‘yan Boys Brigade da aka kashe gab da ranar bikin Ista da ta gabata.

Matasan dai sun mutu ne, bayan motar wani ma’aikacin hukumar tsaro ta Civil Defence ta kwace ma shi, inda ya hau kan su da motar nan take mutane tara su ka mutu.

Har yanzu dai babu cikakken bayani game da musabbabin barkewar rikicin.