Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Barazanar ‘Yan Damfara: Babban Bankin Najeriya CBN Ya Sauke Manhajar E-Naira Daga Play Store Da App Store

Shagunan sayar da manhajojin salula sun sauke manhajar kuɗin intanet na e-naira daga shafukansu kwana uku bayan shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da ita.

Da safiyar Alhamis din nan ne aka gano cewa babu manhajar ta e-Naira a shafukan Play Store (na Android) da kuma App Store (na Apple).

Sai dai wasu da suka sauke manhajar tun farko sun ce tana aiki a wayoyinsu.

Lamarin na zuwa ne daidai lokacin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ankarar da ‘yan Najeriya game da ayyukan wasu bata gari da ke yunkurin Damfarar mutane da sunan e-Naira.

Babban bankin yace wasu sun buɗe wasu shafukan sada zumunta da sunan babban bankin inda suke cewa ana raba kudin e-Naira kimanin Biliyan 50.

CBN ya ce ya samar da kudin ne domin bai wa kowane rukuni na ‘yan Najeriya damar gudanar da harkokin kudinsu cikin sauki bayan ya haramta amfani da sauran kudaden intanet.

Exit mobile version