Home Labarai Barazana: ECOWAS Na Shirin Kara Sanya Wa Mali Takunkumi

Barazana: ECOWAS Na Shirin Kara Sanya Wa Mali Takunkumi

230
0
Shugabannin kungiyar ECOWAS sun sake jaddada bukatar su ta ganin shugabannin sojin Malin sun gudanar da zaben shugaban kasa a watan Afrilu ko kuma a kara sanya musu sabbin takunkumin karya tattalin arziki a watan Janairu.

Shugabannin kungiyar ECOWAS sun sake jaddada bukatar su ta ganin shugabannin sojin Malin sun gudanar da zaben shugaban kasa a watan Afrilu ko kuma a kara sanya musu sabbin takunkumin karya tattalin arziki a watan Janairu.

Bayan taron da shugabannin da suka gudanar a Najeriya, shugaban gudanarwar kungiyar Jean-Claude Brou yace shugabannin sun jaddada matsayin su na ganin an gudanar da zaben shugaban kasar Mali a ranar 27 ga watan Afrilu kamar yadda aka shirya a baya.

Amma dai shugaban sojin Mali Kanar Assimi Goita ya sanar da cewar a karshen watan Janairu mai zuwa zai shaidawa kungiyar ECOWAS shirin sa na gudanar da zabe mai zuwa.

Shugaban sojin Malin yace dalilin dage zaben watan Fabarairun ya biyo bayan taron kasa da ya kaddamar domin baiwa jama’a damar bayyana ra’ayoyin su akan yadda za’a samar da zaman lafiya a kasar.

Ita dai kungiyar ECOWAS ta dakatar da Mali daga cikin ta sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi sau biyu a watan Agustan shekarar 2020 da watan Mayun shekarar 2021 tare da kakabawa shugabannin sojin haramcin tafiye tafiye da kuma rufe asusun ajiyar su.

Goita ya zama shugaban mulkin sojin Mali bayan kifar da gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita a watan Agustan bara.

Leave a Reply