Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Barawon Kayan Lantarki’ Ya Mutu A Cikin Taransufoma A Zariya

Wani mutum da ake zargin barawon kayan na’urar rarraba hasken lantarki ne ya mutu, lokacin da ya shiga cikin na’urar a unguwar Wusasa da ke Zaria a Jihar Kaduna.

Bayanai sun ce, na’urar ita ke ba Unguwar Kuregu da ke Wusasan wutar lantarki, kuma ya mutu ne ya na kokarin yin sata a ciki.

Mazauna yankin ce, Matashin ya gamu da ajalin sa ne da misalin karfe 4:00 na asubahin Lahadin da ta gabata, inda su k ace sun sanar da Mai Unguwa abin da su ka gani kafin daga bisani aka sanar da ofishin yanki na Rundunar ’Yan Sanda da ke Dan Magaji a Zariya.

Daga bisani Jami’an ’yan sanda sun dauki gawar matashin zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika domin ajiya.

Sarkin Wusasa Injiniya Isiyaku ya tabbatar wa manema labarai cewa, ko a makon da ya gabata barayin sun sace kayan daya daga cikin na’urorin da ke unguwar hasken lantarki.

Exit mobile version