Home Home Bankun Sun Canza Ƙa’idar Cirar Kuɗi A ATM Zuwa Naira 200,000

Bankun Sun Canza Ƙa’idar Cirar Kuɗi A ATM Zuwa Naira 200,000

87
0

Banunan kasuwanci sun sun ƙara adadin kudin da mutum zai iya cira a na’urar ATM a rana zuwa Naira dubu 200 maimakon Naira dubu 20 da aka kayyade a baya.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne, Bankin Zenith ya sanar da abokan huldar sa cewa a yanzu za su iya cire kuɗi daga asusun su har Naira dubu 200 a kwace rana daga na’urar ATM, ba tare da la’akari da bankin da aka yi katin ATM ɗin ba.

Sai dai bankin ya ce, dokar da ta hana kowane mutum cirar takardun Naira fiye da Naira dubu 500 daga asusun shi a kowane ta na aiki har yanzu.

Rahotanni sun ce, akwai ƙishin-ƙishin cewa sauran bankuna za su shiga sahun Bankin wajen ɗabbaƙa wannna sabon canjin ƙa’ida duk da dai ba su bayyana ƙudurin ba.

A baya dai bankuna da dama sun sanya takunkumi a kan cire Naira dubu 20 daga na’urar ATM a kowace ranara, ga katinan ATM da ba na bankunan su ba ne.

Leave a Reply