Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Bangar Siyasa: An Kashe Mutum 1 A Karawar Magoya Bayan APC A Jihar Niger

APC

APC

Rahotanni sun kawo cewa wani rikici da ya barke tsakanin yan takarar shugaban karamar hukuma na jam’iyyar APC, a zaben karamar hukuma da za a yi a watan Nuwamba a jihar Niger ya yi sanadiyar mutuwar mutum guda sannan wasu da dama sun jikkata.

Lamarin ya afku ne a hanyar Minna zuwa Bida, ya bayyana yan takarar sun yanki fam din takara a zaben shugaban karamar hukumar Katcha.

Wanda lamarin ya rutse da su Abubakar Nda-Bida, ya kasance magoyin bayan Alhaji Danjuma Eindachi, daya daga cikin yan takarar.

Wasu idon shaida sun bayyana cewa magoya bayan dayan dan takarar wanda aka ambata da suna Alhaji Musa Ishyaku da magoya bayan Emindachi sun kara da juna a gadar kogin Gbako inda lamarin ya afku.

An tattaro cewa mambobin kungiyar biyu sun yi amfani da muggan makamai kamar su adda, takobi, da wukake, inda hakan yayi sanadiyar mutuwar Nda-Bida tare da wasu da dama da suka jikkata

DSP Muhammad Abubakar,

Shugaban jam’iyyar a jihar, Alhaji Jibrin Imam, ya tabbatar da labarin, inda ya bayyana larin a matsayin ta’addanci, kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Muhammad Abubakar, ma ya tabbatar da lamarin, cewa “an kama mutum guda da ke da nasaba da lamarin.

Exit mobile version