Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad
Abubakar III, ya karyata rahoton da ke cewa ya ce jami’in
tsaro su na guje wa ‘yan bindiga, amma su na cin zarafin
mutanen da ‘yan bindigar su ka sace.
Sarkin Musulmi ya karyata rahoton ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren cibiyar hulda da mabiya addinai ta kasa Farfesa Cornelius Afebu Omonokhua ya fitar, inda ya ce bai furta cewa jami’in tsaro su na gujewa ‘yan bindiga, amma su na cin zarafin mutanen da ‘yan bindigar su ka sace ba.
Sanarwar dai, ta na maida martani ne dangane da jawabin da Sultan ya yi lokacin wani taro da ya gudana a dakin taro na Masaukin baki na NICON da ke Abuja.
Sanarwar ta kara da cewa, bayanin da Sultan ya yi a wajen taron, wasu kafafen yada labarai da aka gayyata ba su wallafa bayanin shi daidai ba.
Ta ce bayanin da Sultan ya yi a wajen taron shi ne, idan ‘yan bindiga su ka kai hari cikin al’umma su ka kashe mutane tare da kone gidaje ba a daukar wani mataki akai, inda sai bayan ‘yan bindigar sun kammala aikata ta’asar sai jami’in tsaron su je inda abin ya faru.
You must log in to post a comment.