Matasan Arewacin Najeriya sun bukaci gwamnonin yankin su kwace shagunan duk masu goyon bayan kungiyar ’yan a-warren Biafra ta IPOB a yankin arewa.
Matasan sun bayyana hakan ne a martaninsu ga umarnin IPOB ga mutanen yankin Arewa ta Tsakiya cewa su zauna a gida kar su bude harkokin kasuwancinsu a matsayin goyon baya ga kungiyar.
Sanarwar da kakakin Kungiyar Tuntuba ta Matasan Arewa (AYCF), Yerima Shettima, ya fitar ta ce, “Muna kira ga gwamnonin Arewa da su tabbartar cewa kngiyar ta’addanci ta IPOB ba ta shigo nan yankin ba.
Ya ce Arewa ta dade da fahimtar muhimmancin kiyaye bin doka da oda wajen neman biyan bukatunta a karkashin tsarin dimokuradiyya, saboda haka ba za ta taba biye wa ’yan a fasa kowa ya rasa ba.
A cewar AYCF, tun da gwamnonin yankin Kudu maso Gabas sun gamsu da abin da IPOB take yi a yankinsu, idan sun ga dama su shekara 10 suna ci gaba da zama a gida yadda kungiyar take so, babu abin da ya dami Arewa.
ACF ta soki matakin yin kone-kone ko kashe-kashe da sunan neman biyan bukata, wanda hakan ya saba wa tsarin dimokuradiyya.
Don haka ta bukaci jama’ar Arewa da su guji duk wani yunkuri na tayar da fitina.