Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, Sepp Blatter ya ce an tafka babban kuskure wajen ba Qatar damar karbar bakuncin gasar lashe kofin duniya ta bana da za a fara a wannan watan.
Blatter, mai shekaru 86 a duniya, shike shugabantar hukumar FIFA lokacin da aka baiwa Qatar dammar karbar bakuncin gasar a shekarar 2010 kuma tun bayan bata wannan damar Kasar ke shan suka game da matsayar ta na hana masu auren jinsi gudanar da mu’amular su a lokacin gasar, da kuma zargin cin zarafin ma’aikata ‘yan cirani a kasar.
Blatter ya ce Qatar karamar kasa ce, gasar lashe kofin duniya ya mata girma ta amshi bakuncin sa sannan ya ce ko a lokacin zaben, Amurka ya zaba, sai dai ya dora alhakin bai wa Qatar damar daukar nauyin gasar a wuyan tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Turai Michel Platini.
Wannan ne karo na farko da wata kasa daga yankin gabas ta tsakiya ke samun damar karbar bakuncin gasar a cikin shekaru 92 duk da kasancewar kasashen nahiyar a matsayin ‘yan gaba-gaba da ke zuba makudan kudi a abin da ya shafi kwallon kafa sannan wannan ne karon farko da za a gudanar da wannan gasa a yanayin hunturu.