Kotun Daukaka Kara ta sake bada belin tsohon mai ba shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro Kanar Sambo Dasuki.
Haka kuma, kotun ta umarci gwamnatin tarayya ta biya Sambo Dasuki naira miliyan 5 a matsayin diyyar tsare shi da aka yi, wanda ya kauce wa Tsarin Dokar Kasa Sashe na 35 (6) da ya ba kowane dan Nijeriya ‘yancin walwala.
Kotu dai ta sha bada umarni cewa a saki Sambo Dasuki a kan beli, amma gwamnatin tarayya ta yi biris da umarcin ta.

Yayin yanke hukuncin, kotun ta jingine sharuddan beli na farko da aka nemi ajiye naira milyan 100 daga masu karbar beli mutane biyu, wanda a yanzu aka maida shi zuwa na mai kadarar naira miliyan 100 kawai a birnin Abuja.
Yanzu haka dai kotu ta haramta sake kama Sambo Dasuki a tsare shi, kuma ta ce a duk lokacin da ake neman a yi ma shi tambayoyi a kira shi tsakanin karfe 9 na safe zuwa 6 na yamma amma ba da dare ba.
You must log in to post a comment.