An tsare shugabannin ƙananan hukumomi uku kan badaƙalar Naira miliyan 660 na kwangilar aikin samar da ruwa a Jihar Kano.
Hukumar Yaki da Rashawa da kuma Karɓar Korafi ta Jiahr Kano (PCACC) ta tsare shugabannin ƙananan hukumomin ne bayan da suka amsa laifin karkatar da kuɗaɗen zuwa aljihun su.
Shugabannin kananan hukumomin su ne, shugaban riƙo na Ƙaramar Hukumar Ƙiru, Abdulaziz Sulaiman, da na Bebeji, Basiru Abubakar da kuma takwaran su na Ƙaramar Hukumar Garko, Gambo Isa.
A halin yanzu dai suna can suna amsa tambayoyi a gaban jami’an binciken hukumar tare da wasu mutum 19.
Mutanen 19 sun haɗa da masu muƙamin ma’aji, da manyan shugabannin sashen kula da Ruwa da Tsaftar Muhalli (WASH) da sauran manyan jami’ai a ƙananan hukumomin da badaƙalar ta shafa.
Ana zargin jami’an ne da hannu wajen karkatar da kuɗaɗen a wani lokaci ma har da cirar su a tsaba daga bakuna.