Home Labarai Babu Wata Barazana Game Da Faruwar Babban Zaben 2023, Inji IGP Alkali...

Babu Wata Barazana Game Da Faruwar Babban Zaben 2023, Inji IGP Alkali Baba

87
0

Shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Usman Baba Alkali, ya yi tsokaci game da yiwuwar zaben shekara ta 2023, inda ya ce babu wata barazanar da za ta hana gudanar da zaben.

Usman Baba ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar Olumuyiwa Adejobi ya fitar a Abuja, inda ya ce ya bada tabbacin babu matsala ne biyo bayan nazari da cikakken bincike a kan barazanar da rundunar ta yi.

Alkali ya yi tsokacin ne yayin wata ganawa da mataimakin sakatare na ofishin kula da harkokin miyagun kwayoyi a maaikatar harkokin wajen Amurka Todd Robinson.

Shugaban ‘yan sandan, ya gana da jami’in ne a wajen taron shugabannin ‘yan sanda na Majalisar Dinkin Duniya da aka gudanar a kasar Amurka, inda tattaunawar ta mai da hankali a kan yadda za a inganta tallafi ga shirin horar da jami’an ‘yan sandan Nijeriya.