Home Labaru Babu Wani Matsayi Da Aka Kara Wa Abba Kyari – Garba Shehu

Babu Wani Matsayi Da Aka Kara Wa Abba Kyari – Garba Shehu

466
0
Garba Shehu, Mai Ba Wa Shugaban Kasa Muhammdu Buhari Shawara Na Musamman Kan Harkokin Yada Labarai
Garba Shehu, Mai Ba Wa Shugaban Kasa Muhammdu Buhari Shawara Na Musamman Kan Harkokin Yada Labarai

Fadar shugaban kasa ta yi karin-haske game da zargin cewa an kara wa shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari matsayi a shekara ta 2019.

Mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai da hulda da jama’a Garba Shehu, ya ce Abba Kyari ya na nan a matsayin sa na shugaban ma’aikata kamar yadda a ka sani.

Garba Shehu, ya ce ya kamata a jaddada cewa, Nijeriya ta aro mukamin ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ne daga Amurka, wanda shi ke da alhakin tsara wadanda za su rika ganawa da shugaban kasa.

Ya ce a irin wannan tsari da a ka dade ana amfani da shi, aikin shugaban ma’aikata shi ne, ya zama mai ba shugaban kasa shawara a kan komai, sannan ya jagoranci ma’aikatan sa.

Garba Shehu ya kara da cewa, shugaban ma’aikata ne ya ke tsara yadda ake shiga da fita fadar shugaban kasa, kuma shi ke da alhakin kulla alaka da sauran bangarorin gwamnati. Don haka fadar shugaban kasa ta yi fatali da rahotannin da ke cewa shugaba Buhari ba ya son ganin Ministocin sa ne.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/libertytvnews

Twitter: https://twitter.com/libertytvnews

Instagram: https://instagram.com/libertytvng

Liberty Radio 103.3 FM Abuja Kai Tsaye A Yanar Gizo ??

zeno.fm/libertyradioabuja

Tashar Ƴanci 103.1 FM Kaduna Kai Tsaye A Yanar Gizo ??
zeno.fm/tasharyancikaduna ?

Kira ??? +1-701-719-6971 don suraren (Tashar Ƴanci 103.1 FM Kaduna) kai tsaye ta wayar hannu. Musamman Ga Waɗanda Suke Ƙasar Amurka.

Kuna iya turo mana labari ko shawara a: info@libertytvradio.com

Leave a Reply