Home Home Babu Wanda Ya Kara Farashin Mai A Najeriya – NNPCL

Babu Wanda Ya Kara Farashin Mai A Najeriya – NNPCL

94
0

Shugaban kamfanin mai na NNPC Mele Kyari, ya ce babu wanda ya kara farashin man fetur a Nijeriya.

Mele Kyari, ya musanta iƙirarin da wasu kungiyoyin masu dakon mai su ka yi a baya cewa an ƙara farashin man fetur.

Shugaban kamfanin NNPC ya bayyana haka ne, yayin wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a kan matsalar karancin man fetur da ake fama da ita.

Mele Kyrai, ya kalubalanci duk masu ruwa da tsakin da su ka halarci taron, su bayyana wanda ya ce kara farashin man fetur ko kuma su gabatar da hujjar sun saye shi a sabon farashin da su ka yi ikirari.

Leave a Reply