Home Labaru Siyasa Babbar Sallah: Yau Buhari Zai Tafi Daura Hutu

Babbar Sallah: Yau Buhari Zai Tafi Daura Hutu

432
0
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi Daura na jihar Katsina hutun babbar Sallah har sai hutun ya kare.

Ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da wasu mahimman ayyuka a Katsina kafin ya gama hutun nasa.  

Shugaban kasa ya dade bai je Daura ba, tun lokacin babban zaben da aka yi a cikin shekara ta 2019.

A wani bangare kuma gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Litinin da Talata a matsayin ranakun hutu domin gudanar da bikin sallah babba, inda za a koma kan aiki a ranar Laraba.

Leave a Reply