Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Babbar Magana: Kotu Ta Ba EFCC Izinin Kwace Kadarorin Rochas Okorocha

Rochas Okorocha, Tsohon Gwamnan Jihar Imo

Rochas Okorocha, Tsohon Gwamnan Jihar Imo

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, ta ce ta samu amincewar kotu na kwace kadarorin tsohon gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha da matar sa na wucin-gadi.

Shugaban ofishin hukumar EFCC reshen jihar Enugu Usman Imam ya bayyana wa manema labarai haka, yayin da ya ke jawabi a kan ayyukan hukumar a watanni takwas da su ka gabata.

Usman Imam, ya ce hukumar EFCC ta kara samun sahalewar kotu domin kwace wasu kadarori mallakar tsohon hadimin Rochas Paschal Obi da kuma ‘yar sa.

Ya ce hukumar EFCC ta kwace kadarorin ne har sai wadanda ake tuhuma sun amsa tambayoyi a kan yadda su ka mallake su.

Imam ya kara da cewa, EFCC na son sanin yadda gidauniyar Rochas da wasu kamfanonin sa su ka samu kadarorin su ka kuma maida su na su.

Daga cikin kadarorin da Imam ya ce EFCC ta kwace kuwa akwai katafaren gini mai rukuni 16 da gidaje 96, da Otal, damakarantu biyu, da babban shagon saida kaya, da asibiti, da motoci hudu da wani katafaren shagon cinikayya.

Exit mobile version