Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce Kwamitin Riko na jam’iyyar APC karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya farfado da ruhin jam’iyyar musamman ta bangaren sasanta mutanen da suke rikici da juna a jihohi, wanda ya ce hakan ya kara wa APC karfi a kan wanda take da shi a baya.
Shugaba Buhari, ya bayyana haka ne a jawabin sa na wajen babban taron jam’iyyar APC da ya gudana ranar Asabar dinnan a dandalin taro na Eagle Square dake nan Abuja.
Shugaban kasan ya ce daga cikin nasarorin da jam’iyyar ta samu a baya-bayan nan har da yadda gwamnoni uku masu ci suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APCn.
Buhari ya nuna jin dadin sa kan yadda ya ce a yanzu haka, bayan kammala rajistar ’yan jam’iyya da Kwamitin Rikon ya yi, yanzu APC na da ‘ya’ya fiye da miliyan 41, ya ce hakan ko tantama babu na nuni da cewa APC ce babbar jam’iyya a Najeriya kuma tana da karfin iya lashe kowane irin zabe.
Ya roki a ’ya’yan jam’iyyar su guji kara rura wutar rikicin wanda zai iya fusata wasu, ya kuma ja hankalin sabbin shugabannin jam’iyyar su guji siyasar kudi sannan su ba dukkan ’yan takara damar da ta dace, ta hanyar samar da dimokuradiyyar cikin gida.
Shugaba Buhari ya tunatar da wakilan jam’iyyar, wato daliget cewa su suke da wuka da nama wajen zaben ’yan takara ga jam’iyyar, don haka makomar Najeriya na hannun su, wajen zaba mata shugabanni na gari.