Home Home Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Saman Nijeriya Ya Ziyarci Iyalan Wadanda Su Ka...

Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Saman Nijeriya Ya Ziyarci Iyalan Wadanda Su Ka Rasu

1
0

Babban hafsan hafsoshin rundunar sojin sama ta Nijeriya Air Marshal Hassan Bala Abubakar, ya ziyarci iyalan hafsoshin saman da su ka rasu yayin hatsarin jirgin saman mayakan a jihar Neja.

A ranar Larabar da ta gabata ne, babban hafsan ya sauka a birnin Fatakwal, inda ya yi tattaki zuwa gidajen mamatan ya kuma yi ta’aziyya ga iyalan su.

Air marshall Abubakar, ya ce wannan babban rashi ne da ke zama koma-baya ga rundunar sojin sama, wanda zai dauki rundunar shekaru kafin ta cike gurbin, ya na mai cewa ba za a bar iyalan mamatan su tagayyara ba.

Babban hafsan ya kara da cewa, sadaukar da rayuwar da sojojin su ka yi ba zai taba zama asara ba, don haka rundunar da sauran ‘yan Nijeriya za su cigaba da tunawa da su.