Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Babangida Aliyu Ya Nemi Hukumar Zabe Ta Soke Zabubbukan Kogi Da Bayelsa

Babangida Aliyu, Tsohon Gwamnan Jihar Neja

Babangida Aliyu, Tsohon Gwamnan Jihar Neja

Tsohon gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu na jam’iyyar PDP, ya yi kira ga hukumar zabe ta soke zaben gwamna da aka gudanar a jihohin Kogi da Bayelsa.

Babangida Aliyu ya yi kiran ne, yayin wani taron manema labarai a birnin Minna na jihar Neja, ta bakin jami’in yada labaran sa Bala Bitrus.

Ya ce su na bukatar hukumar zabe da gwamnatin tarayya su soke zabubbukan don wanzar da zaman lafiya da ci-gaban dimokradiyya da kuma adalci.

Tsohon gwamnan ya cigaba da cewa, sun bukaci gwamnatin tarayya ta kafa kwamitocin da za su binciki lamarin cikin gaugawa, tare da zakulo wadanda su ka dauki nauyin lamarin domin yin adalci ba kawai yin Allah wadai da kashe-kashe da halaka kayayyaki da aka yi ba.

Ya ce lokaci ya yi da ya kamata Nijeriya ta fara nazari a kan tsarin zabe, da kuma tabbatar da abubuwan da ya kamata a yi domin tsare dimokradiyya da ainihin manufar ta a dukkan zabubbuka.

Exit mobile version