Home Labaru Ba-Zata: Shugaba Buhari Ya Kara Wa Ministocin Sa Wa’adin Yin Murabus

Ba-Zata: Shugaba Buhari Ya Kara Wa Ministocin Sa Wa’adin Yin Murabus

445
0
Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Yayin da ake sa ran zai rushe ministocin sa a wajen taron majalisar zartawar na wannan makon, shugaba Buhari ya umarci ministocin su cigaba da zama a ofisoshin su domin gudanar da ayyukan su har zuwa ranar Talata, 28 ga watan Mayu.

Shugaba Buhari ya bayyana wa ministocin cewa, wannan shi ne zama na karshe da majalisar ta yi a zangon mulkin sa na farko, amma ya shaida wa ministocin su cigaba da aiki tare da shirin mika aiki ga manyan sakatarorin ma’aikatun su.

A karshe ya bukaci ministocin su mika takardun barin aiki ga manyan sakatarorin a ranar Talata, 28 ga watan Mayu, wato jajibirin ranar da za a sake rantsar da shi a matsayin zababben shugaban kasa karo na biyu.

Leave a Reply