Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar kano ya halarci sallar Idi da Sarki Sanusi ya jagoranta a filin Idi na Kofar Mata da ke birnin Kano, sabanin yadda wasu rahotanni su ka ce Ganduje zai yi sallar idin ne a garin Bichi.
Bisa al’ada dai, Sarki da Gwamna su kan gaisa kafin a tada sallah da kuma bayan idar da huduba kuma hakan ta faru.
Sai dai wata majiya ta tabbatar da cewa, an samu ‘yar hatsaniya yayin da aka kammala sallar idi tsakanin magoya bayan dan takarar jam’iyyar PDP Abba Kabir Yusuf da na gwamna Ganduje.
Rahotanni sun ce dukkan bangarorin biyu sun zaro makamai, lamarin da ya janyo sauran masallata tserewa.
Duk
da ya ke babu wani rahoton cewa an samu wadanda su ka jikkata sakamakon
hatsaniyar, amma an fasa rumfar gilashin da Sarki Sanusi ya ke shiga ciki ya ja
sallah sakamakon rikicin.