Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya ce ba zai taba sadaukar da wata makarantar gwamnati don a samar da kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya a garin Daura ba.
Kranta Wannan: A Kara Kason Kudaden Da Jihohi Ke Samu A Kowane Wata-Masari
Masari ya bayyana haka ne, yayin da kwamitin samar da kwalejin ta kai masa ziyara a Katsina, inda ya bayyana damuwar sa game da tashi wata makaranta don a ba kwalejin wuri, ya na mai cewa sai dai idan har gwamnatin tarayya za ta biya diyya.
Ya ce a matsayin shi na gwamna, babu wanda ya tuntube shi game da sadaukar da wata makaranta don a bada damar samar da kwalejin kimiyya da fasaha, amma idan har haka ne sai an biya su diyya, domin gwamnatin jiha ce za ta sauya wa makarantar da aka karba wuri.
Masari ya kara da cewa, a gaskiya ba su da kudin da za su gina sabuwar makaranta, amma gwamnatin tarayya ta na da su, kuma ba za su iya sallamar daliban makarantar ba, saboda kashi 90 cikin 100 daga cikin su ‘yan Katsina ne.
Don
haka ya ce, idan har an ga akwai makarantar da za a dauke domin yin amfani da
ita wajen kafa kwalejin kimiyya da fasahar babu laifi, amma fa a shirya biyan su
diyya.
You must log in to post a comment.