Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya ce zai yi iyakar
kokarin sa domin ganin an fidda talakawa daga kuncin
rayuwa.
Tinubu ya bayyana hakan ne a tsare-tsaren sa na cika alkawarin kawar da abubuwan da ke barazana ga noma da samar da abinci a Nijeriya.
Majalisar Dinkin Duniya dai ta fitar da rahoton hasashen samun karancin abinci a Nijeriya, musamman a yankin Arewa maso Gabas inda a wasu dazuzzuka ‘yan ta’adda ke yi wa manoma barazana.
Mai taimaka wa shugaban a kan harkokin yada labarai Abdulaziz Abdulaziz, ya ce za a raba wa manoma taki da iri kuma za a fadada dazuzzuka a kuma tsaurara matakan tsaro.
Nijeriya dai kasa ce mai kimanin mutane miliyan 200, inda akasarin jama’a da ke rayuwa a kasa da ma’aunin talauci na Majalisar Dinkin Duniya na samun kasa da dala daya a wuni, yayin da janye tallafin fetur ya kara zafafa kuncin rayuwa.