Home Home Ba Zamu Lamunci Salwantar Rayuka Da Dukiyoyi A Katsina Ba

Ba Zamu Lamunci Salwantar Rayuka Da Dukiyoyi A Katsina Ba

98
0

Gwamnan Jihar Katsina Umaru Dikko Radda, ya kira wani taron masu ruwa da tsaki a kan harkokin tsaro domin tattauna hanyoyin da ya kamata a bi wajen magance matsalar tsaro a fadin jihar.

Masu ruwa da tsakin kuwa  sun hada da shugabannin kananan hukumomin da matsalar tsaro ta shafa, da ‘yan majalisar dokoki ta jihar da shugabannin tsaro da, masu rike da sarautun gargajiya da malaman Addini.

Da yake magana a wajen taron, Gwamna Dikko Radda ya ce an kira taron ne domin zakulo hanyoyin magance kalubalen tsaro a jihar Katsina.

Ya ce gwamnatin sa ta dauki aniyar kafa wata cibiya ta musamman a cikin al’umma mai suna ‘Community Watch’ a Turance, wadda za ta nemo matasa ta ba su horo na musamman domin su bada gudunmuwa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar yankunan su daga hare-haren ‘yan bindiga.

Cibiyar dai za ta hada matasa da jami’an tsaro a dukkan kananan hukumomi 34 da ke jihar, domin inganta tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

Leave a Reply