Home Labaru Ba Za Mu Taba Mantawa Da Marigayi Umaru ‘Yar Adua Ba –...

Ba Za Mu Taba Mantawa Da Marigayi Umaru ‘Yar Adua Ba – Tinubu

113
0

Zababben shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi alhinin
tunawa da marigayi tsohon shugaban kasa Umaru Yar’adua,
wanda ya rasu shekaru 13 da su ka gabata.

Bola Tinubu ya ce, ya na tunawa da abokin sa kuma dan’uwan shi na kud-da-kud a fafutukar tabbatar da dimokuradiyya da shugabanci nagari a Nijeriya.

Ya ce a matsayin shi na abokin marigayin kuma abokin gwagwarmayar siyasa, ba zai manta rikon gaskiya da da kishin kasa da nuna kwarewa a harkar ayyukan Umaru ‘Yar’adua ba, tun daga lokacin da ya zama gwamnan a shekara ta 1999 zuwa 2007, da kuma shugabancin Nijeriya da ya yi daga shekara ta 2007 zuwa 2010.

Tinubu ya kara da cewa, yayin da ya ke shirin karbar ragamar shugabancin Nijeriya, ya kuduri aniyar koyi da nagartattun shugabanni irin su marigayi Umaru ‘Yar’adua, wadanda su ka nuna kololuwar nagarta da sadaukar da kai domin ci-gaban Nijeriya.

Leave a Reply