Hukumar Kidaya ta Kasa NPC, ta musanta rahotannin da ke
cewa za a yi tambayoyi game da Addini a lokacin kidayar da
za a gudanar a watan Mayu.
An dai yada wani sakon murya a manhajar Whatsapp, inda ake kira ga Musulmai su sani cewa za a tambaye su game da addinin su a matsayin wata hanyar rage masu yawa a kidayar da ke tafe.
Sai dai a wata sanarwa da daraktan yada labarai na hukumar Isiaka Yahaya ya fitar, ya ce bidiyon na bogi ne kuma ba su da wani shiri mai kama da haka a lokacin gudanar da kidaya, ya na mai tabbatar da cewa hukumar kidaya ba za ta yi wata tambaya da ke da alaka da Addini ba.
Hukumar NPC, ta ce an dauki matakin cire batun Addini da kabila daga takardar kidayar ne, domin irin tsaurin da batutuwan ke da shi a Nijeriya da kuma kare kidayar daga ce- ce-ku-cen da ba ya da amfani.
Ta ce ta bi diddigi ta gano cewa an soma aikawa da wannan sakon ne a manhajar Whatsapp lokacin kidayar da aka yi a Ghana a shekara ta 2021, an kuma soma yada wannan sakon a Nijeriya ne lokacin da aka yi gwajin kidaya a watan Yuli na shekara ta 2022.