Home Labaru Ba ‘Yan Bindiga Kuɗi: Rundunar Sojin Saman Najeriya Ta Musanta Rahotannin Da...

Ba ‘Yan Bindiga Kuɗi: Rundunar Sojin Saman Najeriya Ta Musanta Rahotannin Da Ake Yadawa

165
0
Rundunar sojin saman Najeriya ta musanta rahotannin da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta da ke zargin ta da biyan ‘yan bindiga Naira miliyan 20 don miƙa mata wata bindigar harbo jirgin yaƙi.

Rundunar sojin saman Najeriya ta musanta rahotannin da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta da ke zargin ta da biyan ‘yan bindiga Naira miliyan 20 don miƙa mata wata bindigar harbo jirgin yaƙi.

Rahotannin da ake yaɗawan sun ce an biya wasu ƴan bindiga a yankin ƙaramar hukumar Jibiya a jihar Katsina kuɗin ne domin su ba rundunar bindigar, wadda suka ce rundunar na fargabar ‘yan bindigar na iya amfani da ita wajen harbo jiragen da ake aiki da su a jihar Katsina.

A sanarwar da ta fitar, rundunar sojin saman ta ce babu ƙamshin gaskiya a rahotannin kuma an ƙirƙire su ne don a ɓata mata suna, sai ta yi kira ga jama’a su yi watsi da labarin wanda ta ce na bogi ne.

Rundunar ta ce babu wani dalili da zai sa ta biya ‘yan bindiga kuɗi a lokacin da take ci gaba da kai masu hari a jihar Katsina da wasu sassan yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Ta kuma bayyana cewa ranar 12 ga watan Oktoban 2021, rundunar ta ƙaddamar da hare-hare biyar a yankin Jibiya da rokoki a wurin da jagoran ‘yan bindigan Bala Wuta da yaran sa ke ayyukan su a Kadaoji.