Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki, ya ce bai aikata wani laifin da a yanzu Hukumar EFCC ke kokarin tuhumar sa da shi ba.
Saraki ya kara da cewa, shi bai shiga kafafen yada labarai ya na cacar-baki da hukumar EFCC ba.
Idan dai za a iya tunawa, a cikin watan Mayu ne hukumar EFCC ta shafa wa wasu gideje jan fenti, tare da ikirarin cewa ta tabbatar Saraki ne ya saye su a hannun Kwamitin Saida Kadarorin Gwamnatin Tarayya.
EFCC ta ce Saraki ya sayi gidajen ne ta hannun kamfanin harkokin danyen mai fetur na Shell.
A wani sabon zargi kuma, hukumar EFCC ta ce Saraki ya kwashi naira biliyan 12 daga asusun Gwamnatin Jihar Kwara, tsakanin shekara ta 2003 zuwa zuwa 2011, lokacin da ya yi gwamnan Jihar. EFCC ta ce, an cire kudaden ne domin Saraki ya biya kudin bashin banki, wadanda ya yi amfani da naira biliyan 1 da miliyan 36 ya sayi gidaje a kan titin Macdonald da ke Ikoyi a Lagos.
You must log in to post a comment.