Home Home Ba Na Da Masaniya Kan Sakin Murja Kunya – Abba Kabir

Ba Na Da Masaniya Kan Sakin Murja Kunya – Abba Kabir

39
0

Gwamnan Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce ba ta da masaniya game da sakin fitacciyar ‘yar TikTok Murja Ibrahim Kunya.

Mai magana da yawun gwamnan jihar, Sanusi Bature, ya shaida cewa gwamna Abba Kabir ba shi da masaniya kan kama Murja, gami da cewa bangaren shari’a ne zai iya ba da bayani kan hakan.

Bature ya ce gwamna Abba Kabir Yusuf ba ya katsalandan ko shiga harkar da ta shafi bangaren shari’a.

Ya kara da cewa, batun bai kai wani al’amari ba da zai kai ga gwamnati ta saka baki, inda ya kara da cewa, gwamna Abba Kabir ba ya nan ya tafi hutu, kuma bai kamata a alakanta shi da wannan karamin al’amari ba.

A karshe Kakakin Gwamnanan ya ce girman kujerar gwamna ta fi a alakanta ta da batun saboda mutane sama da miliyan 20 yake mulka a jihar Kano.

Leave a Reply