Fadar shugaban kasa ta ce, ba ta yi zaben tumun dare ba a
nadin tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje a
matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa.
Ganduje dai ya zama shugaban jam’iyyar APC ne bayan an kwashe makonni ana yada jita-jitar nada shi a kan mukamin.
Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin siyasa Ibrahim Kabir Masari, ya ce gogewar Ganduje a kan dabarun siyasa ne su ka duba wajen dora shi a kan kujerar.
Yanzu dai za a zuba ido a ga tasirin da Ganduje zai yi a kan mukamin, bayan samun targade a zaben dan takarar sa na gwamnan Kano Nasiru Gawuna da Abba Kabir Yusif na jam’iyyar NNPP ya yi nasara a kan sa.