Home Labaru Ba Mu Janye Wa Tsofaffin Gwamnoni Masu Ba Su Tsaro Ba –...

Ba Mu Janye Wa Tsofaffin Gwamnoni Masu Ba Su Tsaro Ba – Rundunar Ƴan Sanda

249
0

Hukumar kula da ‘yan sandan Nijeriya, ta musanta labarin da
ke cewa ta janye jami’an da ke aikin kare wasu tsofaffin
jami’an gwamnati.

A Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce mutane su yi watsi da sanarwar saboda karya ce tsawgwaron ta.

Ta ce a sanarwar da aka fitar, an nuna sa hannun mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai muƙamin DCP, wanda shi kaɗai zai nuna cewa karya ce saboda a irin wannan, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai muƙamin ACP ne ya kamata ya sa hannu.

Muƙaddashin shugaban ‘yan Sandan Nijeriya Kayode Adeolu Egbetokun, ya ce za su gudanar da bincike domin gano waɗanda su ka fitar da sanarwar domin su fuskanci hukunci.

Leave a Reply