Shugaba Biden na Amurka ya yi Alla-wadarai da hukuncin da Kotun Kolin kasar ta yi na cewa tsofaffin shugabannin kasar ciki har da Donald Trump,
na da kariya ‘yar takaitacciya daga gurfanar da su gaban kotu a kan aikata wani mugun laifi.
Shugaban ya ce hukuncin ya sa shi fargaba da tsoro, inda yake jiye wa dumukuradiyyar Amurka.
Da yake mayar da martani game da hukuncin kotun kolin a fadar sa ta White House, Shugaban na Amurka,
ya ce hukuncin karen-tsaye ne ga tsarin nan na doka ta yi aiki a kan kowa.
Mista Biden ya ce a yanzu wannan hukunci zai karfafa wa Donald Trump gwiwa ya yi duk abin da yake so gaba-gadi.
Kazalika ya ce, hukunci ne mai hadarin gaske ga kasar, da zai share fagen saka da mugun zare a nan gaba,
a ce shugaba zai kasance yana da kariya daga gurfana a gaban kotu kan tuhumar aikata mugun laifi, ya ce hakan cin fuska ne ga Amurkawa.