Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Ba A Ga Watan Zulƙi’Ida Ba A Nijeriya

Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi ta ayyana Lahadi a
matsayin ranar 1 ga watan Zulƙi’ida na shekarar hijira ta 1444,
wadda ta yi daidai da 21 ga watan Mayu na shekara ta 2023.

Matakin dai ya biyo bayan rashin ganin jaririn watan a ranar Juma’a da daddare, lamarin da ya sa Asabar din nan ta zama 30 ga watan Shawwal.

Hakan dai ya na nufin an zo ƙarshen watan da Musulamai su ka yi bikin Ƙaramar Sallah a faɗin duniya, wadda ake yi bayan kammala azumin watan Ramadan.

Ranar 10 ga watan Zulhijja bayan Zulƙi’ida, al’ummar Musulamai daga sassan duniya za su taru a birnin Makkah domin gudanar da Ibadar aikin Hajji ta shekarar 1444 ko kuma 2023.

Exit mobile version