Home Labaru Ayyukan Mazabu: Dan Majalisa Ya Bayyana Makudan Kudaden Da Su Ke...

Ayyukan Mazabu: Dan Majalisa Ya Bayyana Makudan Kudaden Da Su Ke Samu

116
0

Wani dan majalisar wakilai daga jihar Adamawa Kwamoti Laori, ya ce kowane dan majalisa ya na samun kason Naira miliyan 100 domin aiwatar da ayyukan mazabar sa.


Dan majalisar ya yi nadamar cewa, saboda rashin aiwatar da kasafi yadda ya kamata, ‘yan majalisar da kyar su ke samun sama da naira miliyan 80 daga cikin 100 da aka ware.


Kwamoti Laori, wanda ke wakiltar mazabar Numan da Demsa da Lamurde na jihar Adamawa, ya dora laifin rashin aiwatar da kasafin yadda ya kamata a kan rashin ci-gaban tattalin arzikin Nijeriya.
Dan majalisar ya bayyana haka ne, yayin da ya zanta da manema labarai a Yola, biyo bayan kaddamar da wasu rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana da wasu ayyuka a Karamar hukumar Numan.

Leave a Reply