Home Labaru Auren Ozil: Shugaban Turkiyya Erdogan Ya Zama Abokin Ango

Auren Ozil: Shugaban Turkiyya Erdogan Ya Zama Abokin Ango

844
0

Tsohon dan wasan tawagar kwallon kafar Jamus, wanda yanzu yake wa Arsenal wasa Mesut Ozil, ya angwance kuma shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ne babban abokin Ango.
Dan shekara 30 wanda yake da usuli da kasar Turkiyya ya janyo cece kuce lokacin da aka ga hoton sa da shugaba Erdogan, lamarin da ya diga ayar tambaya kan karfin kishin kasar sa Jamus, ganin cewa a wayewar garin ranar ce Jamus ta rikito daga gasar cin kofin Duniya ta 2018.
Shugaban na Turkiyya ya isa inda aka yi bikin auren, wato wani otel na kasaita don shaida yadda Ozil zai auri matar sa, wacce ta taba zama mace mafi kyau a Turkiyya, Amine Gulse.
An ga Erdogan, wanda yake ta murmushi tare da mai dakin sa Emine, tsaye kusa da Ozil da amaryar sa yayin daurin auren.
Bayan ya buga wa Jamus wasanni sau 92, har ma da taka muhimmiyar rawa a lashe kofin duniya a shekarar 2014, Ozil, ya bayyana yin murabus daga buga wa Jamus wasa a watan Yulin bara, yana mai zargin jami’an hukumar kwallon kafar kasar da nuna masa wariyar launin fata.

Leave a Reply