Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya kwance wa Sanata Elisha Ishaku Abbo Cliff zani a kasuwa, sakamakon bayyanar wani bidiyon da ke nuna yadda sanatan sharara wa wata mata a wani shago da ke Abuja, lamarin da ya harzuka ‘yan Nijeriya, kuma ya janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sadarwa.
Atiku Abubakar dai ya bayyana bacin ran sa game da wannan lamari, inda ya ce bai ji dadin ganin bidiyon ba, don haka ya ce dole a bar doka ta yi aikin ta.
Ya ce ya na ba sanatan shawara ya gaggauta neman gafarar matar da ‘yan Nijeriya, sannan ya mika kan sa ga hukumar ‘yan sanda. Atiku Abubakar, ya kuma bukaci shugabannin jam’iyyar PDP su tabbatar sun dauki matakin ladabtar da Sanatan, ‘yan sanda kuma su tabbatar sun yi abin da ya kamata a kan shi.
You must log in to post a comment.