Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Atiku Da Obi Sun Yi Ca A Kan Tinubu

‘Yan takarar shugaban ƙasa Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP da takwaran sa na jam’iyyar Labour Peter Obi, sun caccaki shugaba Tinubu bisa ƙin yarda da rahoton ƙarshe da Ƙungiyar Tarayyar Turai  ta fitar a kan zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana a ranar 25 ga Fabrairu na shekara ta 2023

Idan dai za a iya tunawa, a ranar Talata, 27 ga Yuni na shekara ta 2023, Tarayyar Turai ta miƙa rahoton ta game da zaɓen a Abuja, inda babban jami’in sa-ido Barry Andrews, ya ce rahoton ya samo asali ne daga nazarin bin ƙa’idojin da Nijeriya ta ɗauka na shiyya-shiyya da na ƙasa da ƙasa na zaɓukan Demokradiyya.

Sai dai Gwamnatin Tarayya ta bakin mai ba Shugaban Ƙasa Shawara a kan Ayyuka na Musamman Dele Alake ta bayyana rashin ingancin rahoton a cikin wata sanarwa da ta fitar.

Atiku Abubakar ta bakin mai magana da yawun sa, Mr. Phrank Shaibu, ya ce rahoton ya nuna sakamakon zaɓen ba shi ne ainihin abin da ‘yan Nijeriya su ka zata ba. A na shi bangaren, Peter Obi ta bakin mai magana da yawun sa Obiora Ifoh, ya bayyana martanin da Gwamnatin Tarayya ta yi a matsayin ‘magani bayan mutuwa, ya na mai cewa Jam’iyyar Labour ta na bayan rahoton da Tarayyar Turai ta gabatar a kan zaɓen.

Exit mobile version