Home Home Atiku Abubakar Ya Yi Martani Ga Wike Bisa Ikirarin Cewa An Sanya...

Atiku Abubakar Ya Yi Martani Ga Wike Bisa Ikirarin Cewa An Sanya Masa Guba

118
0

An shaida wa tsohon gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike cewa kayan cikin sa sun lalace ne sakamakon yawan tu’ammalin da ya ke yi da barasa, amma ba da guba ba kamar yadda ya yi iƙirari.

Wani hadimin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP Phrank Shaibu ne ya maida ma Wike martani, inda ya buƙace shi da bayyana ta’asar da ya tafka lokacin zaɓen shugaban ƙasa da ya gabata.

Phrank Shaibu, ya ce kamata ya yi Nysom Wike ya fayyace sirrirrukan da ya ɓoye ba wai shirya taron godiya ba, domin bai nuna wata alamar nadama a kan ɗumbin laifuffukan zaɓen da ya tafka ba.

 Idan dai ba a manta ba, a wajen wani taron harkokin coci a birnin Port Harcourt, Wike ya ce kayan cikin sa irin su ƙoda da hanta sun samu matsala a shekara ta 2018, lokacin da ya yi zargin an sanya ma shi guba.

Nysom Wike dai ya ce an sanya ma shi gubar ne a sakatariyar jam’iyyar PDP ta ƙasa, inda ya yi nuni da cewa kowa ma abin zargi ne, sai dai Phrank Shuaibu ya ce yawan tu’ammali da barasa da ya ke yi ne ya yi sanadiyyar lalacewar kayan cikin sa, amma ba guba ba.

Leave a Reply