Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023 mai zuwa, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi alkawarin kirkiro wani shirin bayar da tallafi da ya kai na Naira tiriliyan bakwai a kwanaki 100 na farkon mulkinsa, muddin aka zabe shi.
Ya ce shirin, na kimanin Dalar Amurka biliyan 10, zai mayar da hankali ne wajen tallafa wa kanana da matsakaitan sana’o’i.
Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne, a lokacin da yake gabatar da manufofi da tsare-tsarensa na tattalin arziki ga Najeriya, yayin wani taron ’yan kasuwa masu zaman kansu da Kasuwar Bajekoli, da ’Yan Kasuwa da Masu Masana’antu ta Jihar Legas (LCCI) ta shirya a Legas.
Dan takarar ya kuma ce zai yi wa tsarin tattalin arzikin kasa garambawul ta yadda zai bunkasa, A cewar tsohon Mataimakin Shugaban Kasar, zai dauki matakan gaggawa da za su taimaka wajen rage kowacce irin zirarewar kudi daga lalitar gwamnati ta ba gaira ba dalili, musamman ta wajen biyan tallafi.
Atiku ya kuma ce, zai dakatar da kowanne irin bayar da tallafi ga kadarorin gwamnati, musamman wadanda kwalliya ba ta biyan kudin sabulu.
Atiku ya kuma nuna takaicinsa kan yadda kudaden da Najeriya ke kashewa wajen biyan basusussukan da ta ciyo suka zarta wadanda take samu a watanni uku na farkon 2022, inda ya yi alkawarin yi wa tufkar hanci muddin aka zabe shi.