Home Labarai Atiku Abubakar Ya Bukaci Gwamnati Ta Tallafa Ma Wadanda Ambaliya Ta Shafa

Atiku Abubakar Ya Bukaci Gwamnati Ta Tallafa Ma Wadanda Ambaliya Ta Shafa

68
0

Dan takarar shugababn kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya ce ya damu mutuka da halin da wadanda ambaliyar ruwa ta shafa tun daga kan garuruwa da kasuwanni da makarantu da asibitocin da su ka lalace, ga kuma daidaikun mutanen da matsalar ta raba da muhallin su.

A cikin wani sako da mai taimaka ma shi ta fuskar yada labarai Abdurrasheed Shehu ya raba wa manema labarai, Atiku Abubakar ya yi ma wadanda su ka rasa ‘yan’uwan su sakamakon Ibtila’in ambaliya ta’aziyya.

Atiku Abubakar, ya yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai su samar da shirin taimakon jin-kai cikin hanzari domin bada agaji ga garuruwan da matsalar ta shafa.

Tsohon mataimakin shugaban kasar, ya ce ya kamata wadannan matsalolin marasa dadi su zama izina domin tunkarar matsalar sauyi da kuma dumamar yanayi.

Atiku Abubakar, ya ce wannan lamari ne da ya shafi kowa a kasar nan, don haka kungiyoyi masu zaman kan su su kara kaimi wajen wayar da kan jama’a a kan yadda za su rage matsalar dumamar yanayi da kuma kare Kai daga masifu.