Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Atiku Abubakar Ya Bude Sabon Aiki Mai Mahimmanci A Jihar Bauchi

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, ya ce kwata-kwata shi ba mutum ba ne mai son shirya bikin murnar zagayowar ranar haihuwar sa.

Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a Bauchi, bayan ya buɗe wani sabon titi mai tsawon kilomita 4 da ke kan hanyar Gombe zuwa Maiduguri, wanda aka sanya wa sunan Atiku Abubakar.

Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ne ya raɗa wa titin sunan Atiku, sannan ya gayyace shi domin buɗe shi.

Atiku Abubakar, ya ce ya karanta bayanai masu ratsa jiki na gaishe-gaishen taya shi murnar cika shekaru 75 a duniya, duk da ya ke shi mutum ne da ba ya gudanar bikin murnar zagayowar ranar haihuwar sa.

A jawabin sa bayan bude Titin, Atiku ya ce ya yi matuƙar farin cikin da ba zai iya bayyana irin daɗin da ya ji ba, sannan ya gode wa Gwamna Bala bisa karimcin da ya nuna ma shi na` gayyatar shi domin buɗe ayyuka a Jihar Bauchi.

Exit mobile version