Home Labaru Asiri Ya Tonu: An Kama Mutane 4 Sanye Da Kayan Sojoji Su...

Asiri Ya Tonu: An Kama Mutane 4 Sanye Da Kayan Sojoji Su Na Kokarin Fashi A Banki

919
0

Wasu mutane hudu da ake zargin ‘yan fashi ne sanye da kayan sojoji, sun shiga hannun jami’an tsaro bayan sun yi yunkurin fashi da makami a wani banki.

Jami’an ‘yan sanda a Ibadan na jihar Oyo ne su ka kama mutanen da ake zargin, Wadanda su ka hada wani Matthew Olagoke, da Ahmed Abdulahi, da Johnson Ojo da kuma Adebanjo Bamidele.

Jami’ai na musamman a karkashin rundunar ‘yan sanda ta jihar sun gano shirin miyagun mutanen, inda su ka bibiye su har zuwa Ibadan yayin da su ke kan hanyar su ta zuwa Ekiti su ka kama su.

Kwamishina Kenneth Ebrimson, wanda ya kama wadanda ake zargin ya bayyana wa manema labarai cewa mutanen sojojin bogi.

Haka kuma, an kama su da bindigogi uku, da harsasai 20, da katin shaida uku, da ATM uku, da wayoyi 7 da kuma laya, sannan an gano wanda ya shirya kai harin wani wani a kofur ne a aikin soja mai suna Adebamji Bamgboye, wanda aka kora daga rundunar sojin.