Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Artabu: ’Yan Sanda Sun Kashe ’Yan IPOB 5 A Ebonyi

IPOB esn e1642273204274 1280x720

IPOB esn e1642273204274 1280x720

Akalla ’yan kungiyar IPOB biyar ne aka kashe a wani artabu da da ’yan sanda a Jihar Ebonyi.

’Yan kungiyar sun kai hari da misalin karfe 9:30 na dare a ofishin ’yan sanda da ke Ishieke a Karamar Hukumar Ebonyi.

Sai dai jami’an ofishin sun ci karfin su a wani artabu na tsawon mintuna 30, inda a aka kona motocin.

Rahotanni sun cewa ’yan sandan jihar da sojoji ne suka kai dauki bayan samun kiran gaggawa daga ofishin ’yan sandan.

Wata majiya mai tushe ta ce karar harbe-harben ya tilasta wa mazauna garin guduwa domin tsira da rayukan su.

Majiyar ta ce maharan sun yi kokarin su tsere, amma suka gamu da ajalin su a hanya a hannun jami’an tsaron.

Exit mobile version