Home Labaru Arewa Maso Gabas: Rundunar Sojin Najeriya Ta Kashe ‘Yan Boko Haram

Arewa Maso Gabas: Rundunar Sojin Najeriya Ta Kashe ‘Yan Boko Haram

588
0

Rudunar sojin Operation Lafiya Dole tare da hadin kan dakarun sojin kasar Chadi sun sami nasarar akan ‘yan kungiyar  Boko Haram a wata arangama da suka yi a arewacin jihar Borno.

Kakakin sojin Najeriya, Kanal Sagir Musa, ya bayyana haka, inda ya ce  rundunar sojin sun hallaka yan Boko Haram 27 kuma sun kwato manyan makamai.

Ya ce rundunar ta sami nasara ce a kauyukan Wulgo, Tumbuma, Chikun Gudu, da Bukar Maryam duk dai a jihar Borno.

Kanal Sagir Musa, ya kara da cewar a lokacin  arangamar, an hallaka yan Boko Haram 27 kuma an kwato makamai wadanda suka hada motocin 5  da Babura da Bindiga kirar AK 47 biyar da Bindiga kirar G3 1, da mai carbi 2 da Bindiga mai harbo jirage 2 da Roka 4  Bindiga mai harba kanta 1 da Bindigan gargajiya 1l da Bam na roka 5  da Harsasai 1000 da motar kirar Nissan.

Ya ce ana gudanar da aikin sintiri na musamman a lungunan garin Gamboru-Ngala domin yaki da ‘yan ta’addan masu gudu daga harin da jami’an sojin hadin gwaiwi ke kai musu.

Leave a Reply